BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Ba mu san da kai ba-Guinness World Records ga wanda da ke kokarin kafa tarihin kuka mafi dadewa 

Guinness World Records, kundi da ke bada lambar yabo ta kafa tarihi, ya nisanta kansa da wani dan Nijeriya da ya kusa makancewa bisa yunkurin kafa tarihin yin kuka mafi tsayi.

Tembu Ebere ya yi yunkurin shiga kundin tarihin na duniya ne bayan da ya ɓarke da kuka ba tare da tsayawa ba na tsawon kwanaki bakwai.

A wata hira da BBC a ranar Lahadi, Ebere ya yi ikirarin cewa ya samu makanta ta tsawon mintuna 45 yayin da yake kokarin kafa tarihin.

Ebere ya ce dole ne ya yi gyara wajen yin kukan ta hanyar rage kururuwa hakan ya haifar masa da ciwon kai kuma idanuwansa sun yi luhu-luhu tare da kumburin fuska.

“Dole ne na sake yin dabara kuma in rage kururuwa a kuka na,” in ji shi yayin da ya kara da cewa ya kuduri aniyar yin kuka na mako guda kamar yadda ya tsara duk da matsalolin da ya fuskanta.

Da yake magana a kan mutumin, Guinness World Records ya nisanta kansa da wannan gasa, inda ya kara da cewa ba zai taba amincewa da irin wannan yunkuri na kafa tarihi ba.

“Ba mu taba saka gasar kuka mafi tsayi a tsarin mu ba. Baya daga cikin irin abubuwan da mu ke duba wa, “in ji hukumar ta rubuta.

Leave a Reply