A Najeriya, kwamitin zaben fitar da gwani na masu neman takarar gwamna a jam`iyyar APC ya soke zaben da aka fara a jihar Zamfara sakamakon zargin tafka magudi da tabarbarewar tsaro a lokacin zaben.
A ranar Laraba ne aka fara zaben bayan an yi ta turka-turkar kusan mako guda.
Sai dai gwamnatin jihar ta ce zaben bai soku ba, kuma za ta ci gaba da gudanar da shi kamar yadda BBC ta kalata daga jihar.
Amma ita ma uwar jam’iyyar APC ta kasa ta aike wa manema labarai wata sanarwa tana cewa an soko zaben, kuma za a sanya wata ranar ta daban domin gudanar da shi.
Kwamitin zaben, wanda ya yi jawabi ga `yan jarida a hedikwatar `yan sandan jihar Zamfara, ya yi zargin cewa akwai matsaloli da dama wadanda suka jibanci magudi da tsaro da suka dabaibaye zaben, kuma babu abin da ya fi dacewa face soke shi