Kano Ayau Hausa, Manyan Labarai

An sanya dokar ta baci a Amurka saboda tsananin sanyi

Amurka na fuskantar matsanancin sanyi wanda aka shafe gomman shekaru ba a taba samun irinsa ba.

Ban da tsananin sanyi, akwai wata iska mai karfi daga yankin Arctic na arewacin duniya da ka iya kawo matsanancin sanyi na kasa da ma’aunin Celsius -53.

Jami’ai a jihar Iowa na gargadin mutane da su guji shakar numfashi mai yawa, kuma su rage yin magana idan sun fita wajen gidajensu.

Akalla mutum miliyan 55 ne ake sa ran yanayin matsanancin sanyi zai shafe su.

An ayyana dokar ta baci a jihohin tsakiyar Amurka kamar Wisconsin da Michigan da Illinois, har ma da jihohin da ke kudancin kasar kamar Alabama da Mississippi.

Ana kuma hasashen sanyin zai cigaba da karuwa har ranar Alhamis, jami’ai sun ce sanyi a birnin Chicago zai zarce na yankin Antarctica.

An dai soke fiye da sauka da tashin jiragen sama 1,100 daga ciki da wajen Amurka tun jiya Talata.

Lamarin ya kai har hukumomi a yankin tsakiyar Amurka an rufe dubban makarantu da shaguna har ma da ofisoshin gwamnati.

Sannan hukumomin sun samar wa mutanen da ba su da wurin zuwa wuraren da za su fake daga wannan matsanancin sanyin a biranen Amurka da dama har da jihar Milwaukee.

Leave a Reply