BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

An sako abokan ango da aka sace a Sokoto

A jihar Zamfara da ke Najeriya yau ne ake sa ran masu sana’ar sayar da waya da aka sace za su sake haduwa da iyalansu.

Hakan na faruwa ne bayan sako su da ‘yan bindiga suka yi da maraicen jiya Alhamis.

Ibrahim Kado wanda shi ne shugaban kasauwar sayar da waya ta Bebeji Plaza a Gusau ya tabbatar wa BBC da sako ‘yan kasuwar sai dai bai fadi ko an biya kudin fansa ba.

Ya ce “Alhamdulillahi an sako su, su 29. Sun fito cikin wani yanayi mai ban-tausayi”.

Dangane da ko gwamnati ta sa taimaka wajen karbo ‘yan kasuwar, ya ce “Ba a cewa gwamnati ba ta sa baki wurin kubutar wani ba, amma mu dai alhamdulillahi yara sun fito,”

A cewarsa dukkanin ‘yan kasuwar 29 babu wanda bai samu rauni ko kuma jikkata ba

An dai sako su ne bayan kwashe kusan mako biyu a hannun masu garkuwa da mutanen bayan dauke su a tsakanin garuruwan Tureta da Bakura.

An dai sace su ne a lokacin da suke komawa gida daga wani daurin aure da suka halarta a jihar Sokoto ranar Asabar 11 ga watan Yuni kan hanyarsu ta komawa gida daga daurin Aure.

Leave a Reply