BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

An sace ‘yan China bayan kashe jami’an tsaro a Neja

Wasu ƴan bindiga a Najeriya sun kai hari wata mahakar ma’adanai a jihar Neja da ke arewa maso tsakiyar kasar, inda suka sace ma’aikata ƴan ƙasar China akalla hudu, tare da kashe jami’an tsaro akalla shida wadanda suka kunshi ‘yan sanda da sojoji da kuma ‘yan sintiri na bijilante.

Kwamishinan ƴan sanda na jihar, Bala Kuryas, wanda ya tabbatar wa da BBC labarin ya ce tuni aka tura jami’ai domin ganowa tare da ceto wadanda aka sace a wani yanki na karamar hukumar Shiroro.

Sai dai kuma wata majiya ta sheda wa BBC, cewa sojoji 4 da ‘yan sandan sintiri (mobile) 4 da kuma ‘yan kungiyar sintiri biyu aka kashe a harin.

Ba a dai san takamaimai wadanda suka kai harin ba, amma daman jihar Naija, na daya daga cikin jihohin kasar da ke fama da matsalar tsaro ta barayin daji masu satar mutane domin karbar kudin fansa.

Baya ga mayakan kungiyoyin masu ikirarin jihadi, wadanda a wani lokacin kan hada kai da ‘yan bindiga masu satar mutane.

Jihar Neja da wasu jihohin a arewacin Najeriyar da suka hada da Zamfara da Nassarawa na da arzikin ma’adanai da suka hada da zinariya, abin da kan kai ‘yan kasar China aikin hakarsu.

Leave a Reply