GAJERAN LABARI, Kano Ayau Hausa

An sace sabon DPO na Birnin Gwari a hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna

’Yan ta’adda suna yi garkuwa da sabon DPO na ’yan sanda da aka tura Birnin Gwari da ke Kaduna.

Rahotannin sun ce an sace dan sandan ne a hanyarsa ta zuwa Birnin Gwari domin  fara aiki a sabon ofishinsa a matsayinsa na sabon DPO a garin na Birnin Gwari.

An ce an sace dan sandan ne da misalin karfe 9 na safiyar yau Litinin, duk da cewa har zuwa lokacin hada labarin ba a tantance ko shi kadai ne yake tafiyar ba, ko kuma tare da rakiya yake.

Kakakin Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ya ce zai bincika sannan ya yi cikakken bayani.

Leave a Reply