’Yan ta’adda suna yi garkuwa da sabon DPO na ’yan sanda da aka tura Birnin Gwari da ke Kaduna.
Rahotannin sun ce an sace dan sandan ne a hanyarsa ta zuwa Birnin Gwari domin fara aiki a sabon ofishinsa a matsayinsa na sabon DPO a garin na Birnin Gwari.
An ce an sace dan sandan ne da misalin karfe 9 na safiyar yau Litinin, duk da cewa har zuwa lokacin hada labarin ba a tantance ko shi kadai ne yake tafiyar ba, ko kuma tare da rakiya yake.
Kakakin Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ya ce zai bincika sannan ya yi cikakken bayani.