Kano Ayau Hausa, Labarai

An kona makiyaya biyu da ake zargi da garkuwa da mutane a Kaduna

Wani dandazon mutane ya yi wa wasu makiyaya kisan rubdugu a Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya bisa zargin suna da alaƙa da hare-haren ‘yan fashin daji.

Jami’an tsaro sun bayyana cewa mutanen sun ƙwace makiyayan biyu daga hannun ‘yan sanda kuma suka kashe su tare da ƙona gawarwakinsu a yankin Birnin Gwari.

Lafiyata ƙalau kuma ba zan janye daga takara ba – Bola Tinubu

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya yi Allah-wadai da kisan cikin wata sanarwa da Kwamashinan Tsaro Samuel Aruwan ya fitar a yau Asabar.

“Dandazon mutanen sun kashe tare da ƙona makiyayan duk da cewa babu wata hujja da ke nuna cewa suna da hannu a hare-haren ‘yan bindigar,” a cewar sanarwar kamar yadda BBC ta ruwaito.

Gwamnan ya umarci ma’aikatar tsaro ta jihar ta haɗa gwiwa da jami’an tsaro don a haƙurƙurtar da ‘yan uwan makiyayan da zimmar kare harin ramuwar gayya.

Leave a Reply