A yau Alhamis an yi jana’izar mutane biyar da aka kashe a rikicin zaben jihar Zamfara.
An dai kashe mutanen ne a cibiyoyin zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a jihar da aka fara tun jiya Laraba.
Jama’ar jihar da dama sun halarci jana’izar mutanen da aka kashe inda wasu daga cikin ‘yan takarar Gwamnan suka halarci sallar jana’izar ciki har da mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Wakkala Muhammad.
Wadanda suka samu raunuka akasarin su matasa, an dai sari wasu da adda lokacin rikicin.