A ranar Asabar da ta gabata ce dubun wani sojan-gona mai mukamin Kanar ta cika, bayan da aka kama shi a Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.
Ana zargin sojan-bogin ne da taimaka wa ’yan ta’addan yankin Birnin Gwari da suka dade suna addabar mutanen yankin.
Aminiya ta gano cewa sojan-gonar ya kwashe shekara biyu yana yawo a yankin a matsayin Kanar din soja, har sai da dubunsa ta cika.
Shugaban wata kungiya da ke kare muradun yankin Birnin Gwari da yayata bayanai a kan lamuran tsaro mai suna Ibrahim Abubakar Nagwari ne ya tabbatar da kama wanda ake zargin a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.
Ya ce wani soja mai suna Kyaftin Buhari Adamu ne ya kama sojan-bogen a wani otel mai suna Kada a Birnin Gwari, kafin ya mika shi ga shugaban sojoji da ke aiki na musamman a yankin mai suna Manjo Muhammad Gana.
“An kama sojan-bogen ne a otel din Kada da ke kusa da dam din Bagoma, inda yake zaune kusan shekara biyu. Tuni an mika shi ga Manjo Muhammad Gana, wanda shi ne jami’i mai kula da yankin Birnin Gwari. Haka kuma ana zargin wanda aka kama yana mika wa ’yan ta’addan yankin bayanan sirri ne,” inji shi.
Nagwari ya yi kira ga rundunar sojin kasar nan da ta bayyana wa al’umma sunan sojan-bogen da kuma asalinsa. Har ila yau ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta sanya dokar ta baci a yankin Birnin Gwari domin a samu magance matsalar ’yan ta’addan da ke addabar jama’ar yankin.