Kano Ayau Hausa, Labarai

An janye karar da aka kai NNPP tsagin Kwankwaso

Tsohon shugaban jam’iyyar NNPP na Jihar Kano, da sakatarensa Usman Garko, sun janye ƙarar da su ka kai shugaban jam’iyyar na yanzu, Umar Doguwa.
Wata Babbar Kotun Kano, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Sanusi Ma’aji ta sanya ranar 26 ga Afrilu, 2022, domin sauraren ƙorafin da su ka shigar a kan Shugabannin jam’iyar, ƙarƙashin Umar Doguwa.
Mutanen biyu dai sun shigar da ƙara ne, su na masu neman a dakatar da shugabannin jam’iyyar NNPP, biyo bayan rusa shugabannin jam’iyar da Habib ɗin ya jagoranta.
Habib da Garko sun nemi kotun, gami da dai sauran Ƙorafe-ƙorafe, da ta aiyana zaɓen shugabannin da Doguwa ke jagoranta a matsayin haramtacc, wanda ya saɓawa doka, kuma maras amfani da tasiri kuma ba shi da wani tasiri, inda su ka kuma nemi da kotun ta da ayyana cewa shi ne sahihin shugaban jam’iya.
Sai dai kwatsam, a wani sauyin shawara Habib da Garko sun shigar da wata takarda, mai kwanan wata 26 ga Afrilu, 2022, kan dakatar da ƙarar da su ka shigar a kan NNPP, Doguwa (da sauran mambobin kwamitin zartarwa na jihar Kano) da INEC.
A cikin sanarwar da DAILY NIGERIAN ta samu a yau Laraba, masu shigar da kara sun dogara ne da doka mai lamba 23 na doka ta 1 ta babbar kotun jihar Kano ta shekarar 2014.
Sai dai Habib bai bayyana dalilansa na janye karar ba.

Leave a Reply