Kano Ayau Hausa, WASANNI

An dakatar da wasan kwallon qafa a Jamus domin dan wasa ya yi buda-baki

Gasar ƙwallon ƙafa ta Bundesliga a ƙasar Jamus ta ga wani sabon abu a wasannin tsakiyar mako, yayin da Ausburg ta karbi bakuncin Mainz a filin wasa na WWK a ranar Laraba da ta gabata.
Ana tsaka da wasan ne, daidai minti na 65, sai alƙalin wasan, bayan an miƙa buƙatar, ya tsayar da wasan domin Moussa Niakhat, ɗan kungiyar Mainz ɗin ya yi buɗe-baki.
Na’urorin ɗaukar hoto mai motsi sun ɗauki lokacin da a ka ƙyale mai tsaron bayan na Mainz ya sami abin da zai sa a bakinsa cikin sauri, wanda hakan ya daɗaɗa wa ƴan kallo su ka riƙa tafi da shewa daga kan benayen filin wasan.
A na tsayar da wasan ne sai mai tsaron ragar Mainz, Jeffrey Gouweleeuw ya garzayo da gudu ya miƙo wa Niakhat, wanda Musulmi ne ɗan ƙasar Faransa, lemo da ruwa domin ya jika maƙoshinsa.
Yana bashi kuwa ya daga robar lemon ya sha, ya kuma karɓi ta ruwan ita ma ya ɗaɗɗaka cikin gaggawa kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta ruwaito.
Bayan ya kammala sha ne, ya jefa robin bayan fili, inda ya yi gudu wajen alƙalin wasa ya miƙa masa hannu su ka tafa, a wani yanayi na godiya ga shi alƙalin.
A halin yanzu dai hotuna sun gauraye kafofin sada zumunta inda su ke nuna lokacin da aka dakatar da wasan na Bundesliga na wucin-gadi tsakanin Ausburg da Mainz don ba da damar Niakhat ya sha ruwa.
Kungiyoyin biyu sun fafata ne da yammacin Larabar, inda mai masaukin baki Ausburg ta yi nasara da ci 2-1 a ragar Gouweleeuw da Ruben Vargas, yayin da Silvan Widmer ya ci wa masu ziyara kwallo ɗaya.
Ko a bara ma, an yi haka a gasar Firimiya ta Ingila, inda alkalan wasa su ka riƙa tsayar da wasanni su ka baiwa ƴannwasa irin su Paul Pogba, Wisley Fofana, Aboubacar Kyoteh, Sadio Mane da sauransu, damar su yi buɗe-baki a na tsaka da wasa.

Leave a Reply