BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

An dakatar da daukar ‘yan sanda

Hukumar da ke kula da batutuwan da suka shafi aikin dan sanda a Najeriya (PSC) ta dakatar da aikin daukar sababbin kuratan ƴan sanda.

Hukumar ta dauki wannan matakin ne kasa da sa’a 24 bayan da sufeto-janar na ƴan sandan Najeriya Usman Baba ya bayyana bacin ransa kan wani talla da aka wallafa kan daukan masu sha’awar aikin dan sandan.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan Najeriya Olumuyiwa Adejobi ya fitar, sufeto-janar din ya bukaci ƴan Najeriya su yi watsi da tallan da aka wallafa a wsu manyan jaridun kasar.

A nata bangaren, hukumar ta PSC ta ce akwai wani rashin fahimta tsakaninta da rundunar ƴan sandan Najeriya.

Kakakin hukumar Ikechukwu Ani ya ce nan ba da dadewa ba za a sasanta kan wannan batun. Ya kuma ba masu sha’awar aikin da su jinkirta zuwa wani lokaci nan gaba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar ta PSC ta taba kai karar rundunar ƴan sandan Najeriyar da tsoho sufeto-janar Mohammed Adamu kan gudanar da aikin daukan kuratan ƴan sanda 10,000 a 2019, sai dai daga baya sun sasanta, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Leave a Reply