BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Amurka ta ba ‘yan kasa damar mallamar bindiga

Kotun Ƙolin Amurka ta soke wata dokar New York ta taƙaita mallakar bindiga.

Dokar ta buƙaci ƴan ƙasar da ke son lasisin mallakar bindiga da su gabatar da gamsasshiyar hujjar su ta son ɗaukar makaman, da kuma tabbatar da cewa suna fuskantar hatsari.

Dokar da ta sanya waɗancan matakan ta ci karo da damar mallakar makamai da kundin tsarin mulki ya tanada, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Sannan hukuncin Kotun Ƙolin ya yi tasiri a kan takaita mallakar makaman da ke aiki a wasu jihohin tare da faɗaɗa damar mallakar bindigogin.

Alkali Clarence Thomas, wanda ya yanke hukuncin a madadin alkalai shida mafi rinjaye masu ra’ayin mazan jiya, sun ce Amurkawa na da damar mallakar “bindiga” don kare kawunansu.

Sai dai sauran alkalan uku masu sassaucin ra’ayi Elena Kagan da Sonia Sotomayor da Stephen Breyer ba su goyi bayan hukuncin ba.

Leave a Reply