WASANNI

Alexis Sanchez ya fara tunanin komawa Arsenal

Rahotannin da ke fitowa daga kulob din Manchester United na Ingila sun nuna Aledis Sanchez, ya fara tunanin komawa kulob dinsa na da wato Arsenal a watan Janairun badi.

Sanchez ya canja sheka daga Arsenal zuwa United ne a kakar wasan da ta wuce a wata musaya da kulob din biyu suka yi inda Sanchez ya koma United yayin da Henrik Mkhitaryan ya koma Arsenal, wannan canji bai yi wa dan kwallon dadi ba ganin yadda tauraruwarsa ta yi kasa.

Hakan ta sa kocin United Jose Mourinho ya yi masa gargadin muddin bai canja hali ba, ba zai sake sanya shi a wasa ba.

Wannan kalami da kocin ya yi wa dan kwallon ta sa Sanchez ya fara tunanin barin kulob din a karshen kakar wasa ta bana, ko kuma a watan Janairu idan aka bude kasuwar cinikin ’yan kwallo.

Kulob da dama ciki har da na PSG da ke Faransa da Real Madrid da ke Sifen na daga cikin wadanda ake rade-radin suna zawarcin Sanchez.  Kamar yadda wani rahoto ya nuna akwai yiwuwar dan kwallon ya koma Arsenal.

Leave a Reply