Kano Ayau Hausa, NISHADI

Alan Waka da Abbale sun tsaya takarar Majalisar Wakilai a Kano

‘Yan Kannywood Adam Abdullahi Adam wanda aka fi sani da Daddy Hikima ko kuma Abbale, da fitaccen mawaki, Aminu Ladan Abubakar da aka fi sani da Alan Waka, da kuma Naziru Dan Hajiya sun fito takara a kakar siyasar 2023 mai zuwa.

Duka su uku sun fito takara ne a karkashin jamiyyar ADP, wacce dan majalisar Birnin Kano da Kewaye, Sha’aban Ibrahim Sharada, yake yi wa takarar Gwamna a jihar Kano kamar yadda muka kalato daga Aminiya

An bukaci ‘yan sanda su binciki Gwanja da Safara’u da sauransu

Daddy Hikima (Abbale)

Ainihin sunansa shi ne Adam Abdullahi Adam. Jarumin wanda ya yi suna a irin matsayin da ya ke fitowa na dan daba a fina-finan na Kannywood, ya fito a wasu fina-finai da yawa.

Daga cikin irin wadannan fina-finai akwai A duniya da Farin Wata da Haram da Na Ladidi da kuma Sanda.

Jarumin ya tsaya takarar Majalisar Wakilai ne, a mazabar Kumbotso ta jihar Kano.

Aminu Abubakar Ladan ALA

Alan waka kamar yadda aka fi kiransa, dan asalin unguwar Tudun Murtala ne, ya kuma yi rubutun littafan labaran soyayya kafin ya shiga harkar waka.

Cikin littattafan da ya rubuta akwai Cin Zarafi da Bakar Aniya da Sawaba da Cin Fuska, da Jirwaye da kuma Tarzoma.

Ya kuma soma waka ne tun yana dalibi a makarantar Islamiyya a inda basirarsa ta fito, kuma a yanzu ya yi shuhura, har ta kai ana nazarin wakokinsa a makarantun gaba da sakandare a ciki da kuma wajen kasar nan.

Ala ya fito takarar kujerar Majalisar Wakilai ne a mazabar Nassarawa da ke jihar Kano.

Naziru Dan Hajiya

Naziru haifaffen garin Jos ne a jihar Filato. Ya shahara ne wajen shirya fina-finai a inda ya shirya sama da guda 20.

Cikin fina-finan da ya shirya akwai Bahaushiya, Baya da kura da Gamdakatar da Halisa da kuma Al’ajabi.

Naziru shi ma ya tsaya takarar kujerar Majalisar Wakilai a mazabar Kura, Madobi da Garun Malam a jihar Kano.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ‘yan Kannywood ke tsunduma harkar siyasa ta hanyar tsayawa takarar zabe kai tsaye ba, musamman a jihar Kano.

Ko a zaben 2011, jarumi Hamisu Lamido Iyantama ya taba tsayawa takarar Gwamnan Kano a zaben a karkashin jam’iyyar ND.

Leave a Reply