Big Story, GAJERAN LABARI, Kano Ayau Hausa

An bukaci ‘yan sanda su binciki Gwanja da Safara’u da sauransu

An maka shahararrun mawaƙan zamani na Arewa da fitattun jaruman TikTok a gaban Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke yankin Bichi a Kano bisa zargin rashin tarbiyya.

Duk da cewa ba DAILY NIGERIAN ba ta samu kwafin ƙarar ba, amma majiyoyi sun ce laifuffukan sun haɗa da wakokin rashin tarbiyya da rawar Tiktok da ke da alaƙa da lalata tarbiyyar al’umma.

Sai dai DAILY NIGERIAN ta samu kwafin wasikar da kotun shari’ar Musulunci ta rubuta wa ƴan sanda na neman a binciki koke-koken da ke gaban masu gabatar da ƙara.

Wadanda aka zayyana a wasikar da aka aika wa kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano sun hada da 442, Safara’u, Dan Maraya, Amude Booth, Kawu Dan Sarki, Ado Gwanja, Murja Kunya, Ummi Shakira, Samha Inuwa da Babiyana.

“Sakamakon karar da Muhd ​​Ali Hamza Esq, Abba Mahmud, Esq, Sunusi I. Umar Esq, Abba, A.T Bebeji Esq, B.I Usman Esq, Muhd ​​Nasir Esq, L.T Dayi Esq, G.A Badawi & Badamasi Suleiman Gandu Esq su ka gabatar.

“Alkali mai shari’a na Babbar Kotun Shari’a na Bichi a Kano ya umurce ni da in rubuta tare da neman ku da ku gudanar da bincike a kan wadanda ake zargin a sama domin daukar matakin da ya dace.

“An maƙala kwafin takardar korafin don ƙarin bayani. Ka huta lafiya,” in ji wasiƙar, wacce rijistaran kotun, Aminu Muhd ​​ya sanya wa hannu.

Leave a Reply