Kano Ayau Hausa, Labarai

Ahmed Musa ya kafa sabon tarihi

Kyaftin ɗin tawagar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya Super Eagles ya kamo tarihin da Zidane ya kafa na yawan buga wa ƙasarsa wasa.
Ahmed Musa – wanda shi ne ya fi kowa buga wa Najeriya wasa – ya buga wasansa na 108 a karawar da Super Eagles ta doke Guinea-Bissau da ci 1-0 ranar Litinin.
Ɗan wasan wanda ya fara taka wa Najeriya leda a shekarar 2010 na daga cikin tawagar ƙasar da ta lashe kofin ƙasashen Afirka a shekarar 2013.
Da wannan wasa ɗan wasan ya kamo tarihin da tsohon ɗan wasan Faransa Zinedine Zidane, da ɗan wasan Jamus Jurgen Klinsmann da kuma Tim Cahill na Ingila waɗanda duka suka taka wa tawagogin ƙasashensu wasa sau 108.
Ɗan wasan mai shekara 30 ya zarta Patrick Vieira da Frank Lampard a yawan wasannin da suka taka wa ƙasashensu wasa
Ahmed Musa ya ci wa Najeriya ƙwallaye 16, kuma shi ne ɗan wasan da ya fi kowanne ɗan wasan ƙasar zura ƙwallo a gasar Kofin Duniya inda ya zura kwallaye huɗu.
Ya kuma zura ƙwallaye 92 a ƙungiyoyi daban-daban da ya buga wa wasa.

Leave a Reply