Kano Ayau Hausa, Labarai

Abin da ya sa na fita daga PDP – Rabiu Sulaiman Bichi

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kano Rabiu Sulaiman Bichi, ya bayyana dalilansa na ficewa daga jam’iyyar zuwa jam’iyya mai mulki ta APC a jihar.

A ranar Talatar nan ne dai wasu rahotanni suka bayyana cewa ya raba gari da PDP da ke karkashin jagorancin Rabi’u Musa Kwankwaso, tare kuma da jingine matsayinsa na shugabancin jam’iyyar a jihar Kano.

Sai dai bai bayyana hakan ga al’umma ba sai a ranar Laraba da yammaci.

A wata hira da ya yi da BBC Hausa, ya ce ya koma APC ne saboda shugabannin jam’iyyar ne suka nemi ya koma domin bayar da gudummawarsa don ciyar da jihar Kano gaba.

Wannan dai na zuwa ne bayan hukuncin da Kotun Kolin Najeriya ta yanke a ranar Litinin na korar karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP ta a Kano wato Abba Kabir Yusuf ya shigar.

Wasu na ganin wannan ne dalilin da yasa ya bar PDPn da kuma neman mukami a APC.

Amma ya musanta hakan a hirarsa da BBC.

”Ita siyasa ta gaji haka, mutum in yana ganin zai ci gaba a wurin da yake to yana da ‘yancin yin hakan, in kuma yana ganin zai canza nan ma yana da ‘yanci, ai da muna cikin gwamnati muka ajiye.” ~ Inji Shi

Sai dai bai ce komai ba a lokacin da BBC ta tambaye shi ko ya yi shawara da tsohon mai gidansa jagoran Kwankwasiyya na PDP Rabi’u Musa Kwankwaso kafin yanke hukuncin ficewa.

Leave a Reply