BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Abin da ya sa ba mu janye yajin aiki ba-ASUU

An gaza cimma matsaya a taron da gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi da kungiyar malaman Jami’o’i ta ASUU a ranar Talata.

Hakan na nufin yajin aikin da kungiyar ke yi a yanzu haka zai ci gaba.

Bayanai sun nuna cewa wakilan kungiyar da suka gana da kwamitin Farfesa Nimi Briggs, a hukumar kula da Jami’oi ta kasar sun je wajen da cikakken fatan za a warware matsalolin da suka sanya su tsunduma cikin yajin aikin da suka shafe watanni shida suna yi.

ASUU ta ce kwamitin da Farfesa Nimi Briggs ke jagoranta bai je musu da wani sabon abu ba a taron.

A maimakon haka kwamitin ya bukaci ‘yan kungiyar da su dakatar da yajin aikin da suke, tare da alkawarin cewa za a sanya bukatunsu a cikin kasafin kudin 2023.

Rahotanni sun ce an shafe sa’oi uku a wajen taron, amma ba bu wata matsaya da bangarorin biyu suka cimma.

A ranar 14 ga watan Fabrairun 2022 ne, kungiyar ta ASUU ta fara yajin aikin saboda bukatar gwamnatin tarayya ta bcika musu wasu bukatunta.

Daga cikin bukatun akwai inganta jin dadi dav walwalar ‘ya’yan kungiyar da kuma basu ‘yancin cin gashin kansu da sauransu.

Leave a Reply