BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Abin da ya sa Atiku ya je Amurka

Karshen dai tika-tika-tik. Bayan cece- kucen da aka rinka yi a Najeriya akan cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Abubakar ba zai iya shiga Amurka ba, a karshe dai ya shiga.

‘Yan Najeriya musamman dai ‘yan jam’iyya mai mulki ta APC sun ta kalubalantar shi a kan cewa idan ba tsoro ba yaje kasar Amurka.

Atiku Abubakar dai tsohon mataimakin shugaban kasa ne a Najeriya kuma a yanzu haka dan takarar shugabancin kasar ne a karkashin inuwar jam’iyyar adawa ta PDP.

Sau da dama ana ta rade-radin cewa idan Atiku yaje Amurka zai fuskanci dauri sakamakon wani laifi da ya tafka a kasar kamar yadda BBC ta kalato.

Ya sha dai musanta wannan zargin a lokuta da dama inda ya bayyana cewa babu wanda ya taba kama shi da laifin aikata rashawa.

Sai dai a ranar Alhamis 17 ga watan Junairu ne kwatsam aka ga hotunan Atiku suna yawo a shafukan sada zumunta wadanda ke nuna cewa ya je Amurka.

An dai ga tsohon mataimakin shugaban kasar ne tare da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki a cikin hotunan.

Dan takarar shugaban Najeriya na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, yana ziyara a Amurka ne domin ganawa da manyan jami’an gwamnati da ‘yan kasuwan kasar da kuma ‘yan Najeriya mazauna Amurka.

Sai dai a wata hira da Atiku ya yi da BBC a kwanakin baya, ya bayyana cewa ya nemi izinin shiga Amurka, amma an hana shi.

Ko da aka tambaye shi a kan batun gidansa na Amurka da aka yi gwanjonsa sai ya bayyana cewa gidan matarsa ne da ya saya mata a kasar kuma ita ta sayar da gidan nata.

A hirar dai ya bayyana cewa ba dole ba ne sai mutum ya je Amurka kafin ya zama shugaban kasar Najeriya, babu inda aka fadi haka a kundin tsarin mulki, in ji Atiku.

Tun bayan isar Atiku Amurka, tuni dai mutane da dama suke sharhi suna tafka muhawara a shafukan sada zumunta akan wannan batu.

Da dama wasu daga cikin magoya bayansa a shafukan sada zumunta suna ta murna a kan cewa gwaninsu ya shiga Amurka, wasu kuma har yanzu ba su yarda ba inda suke ganin cewa kamar hada hotunan aka yi.

Leave a Reply