Kano Ayau Hausa, Manyan Labarai

Abin da ya sa aka daina jin duriyata – CP Wakili

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano CP Mohammed Wakili ya ce abin da ya sa aka kwana biyu ba a ji dukriyarsa ba.

Ya ce yana nan “daram dam kuma muna aikinmu a baya an rika jin duriyarsa ne saboda lokacin zabe ne,” kamar yadda ya shaida wa wakilinmu Khalifa Dokaji a Kano ranar Laraba.

“Ana gwagwarma neman zabe akwai abubuwa da dama wadanda na tsaro ne wanda yake dauke hankalin jama’a.”

“Saboda haka na bukatar a ji tabbaci, za a yi lafiya za a gama lafiya…wanda yake duk yanzu babu su,” in ji shi.

Daga nan ya ce yana nan lafiya lau kuma yana aikinsa yadda ya kamata, kamar yadda BBC ya ruwaito.

Batun shaye-shayen a jihar Kano

CP Wakili ya ce tun da aka kammala zabe zuwa yanzu sun kama ‘yan daba wadanda suke kurkuku fiye da 930.

Ya ce masu tu’ammali da miyagun kwayoyin sun suaya salo, “amma a yanzu haka muna binciken wani muhimmin batu.”

Leave a Reply