Shugaban Gwamnonin APC, Rochas Okorocha ya bayyana dalilin da ya sa wasu gwamnonin APC suka halarci fadar shugaban kasa domin tattaunawa da shugaba Buhari.
Da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa, Rochas ya ce, “mun zo ne domin tattauna a kan matsalolin da aka samu zaben fidda gwani na jam’iyyarmu domin samun maslaha. Jam’iyyar APC jam’iyyar adalci ce da gaskiya. Don haka ne muka bukata a yi abin da ya dace ta hanyar barin kowa ya shiga a fafata da shi a zaben.”
A dazu ne muka buga labarin cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana wata ganawar sirri da wasu gwamnoni na APC.
Gwamnonin su ne: Abiola Ajimobi da Jihar Oyo da Ibikunle Amosun na Jihar Ogun da Rochas Okorocha na Jihar Imo da Abdul’aziz Yari na Jihar Zamfara da Atiku Baugudu na Jihar Kebbi da Sani Bello na Jihar Neja da Simon Lalong na Jihar Failato da Rotimi Akeredolu na Jihar Ondo da Tanko Almakura na Jihar Nasarawa.