Kano Ayau Hausa, Siyasa

Abdulmumini Jibrin ya fice daga APC

Fitaccen dan siyasa kuma tsohon dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin ya fice daga Jam’iyyar APC.

Abdulmumini ya bayyana hakan be a shafukansa na sadarwa, inda ya ce “Nayi wa APC iya kokari na lokaci yayi da zan yi gaba. Zan sanar da sabuwar jamiyyar da zan shiga cikin sa’oi 24 In sha Allah. Zanyi cikakken bayani bada jimawa ba. Hon Abdulmumin Jibrin”

Abdulmumini jigo ne a APC bangaren Gwamna Ganduje, kuma shi ne kan gaba wajen tallata takarar Bola Tinubu na shugabancin kasa.

Leave a Reply