Kano Ayau Hausa, Siyasa

2023: ‘Yan Najeriya ne suka ce in sake tsayawa takara-Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abukabar ya ce ƴan kasar ne suka buƙaci ya tsaya takarar shugaban ƙasa a shekarar 2023.

Atiku ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata kwana guda kafin ya ayyana takararsa a hukumance.

Atiku wanda ya sha fitowa takarar shugaban ƙasa ya ce zai tsaya takara ne a 2023 domin kawo wa ƴan Najeriya sauƙi kan matsalolin da suke fuskanta musamman abin da ya kira “rashin haɗin kan ƙasa.”

Da aka tambaye shi ko yaya zai yi da sauran abokanan takararsa na jam’iyar PDP, sai Atiku ya ce ba su da wata matsala a jam’iyyar domin kuwa idan suka zauna za su fitar da ɗan takara cikin ruwan sanyi.

“Idon muka shiga daki muka zauna zamu fita mu kuma fitar da ɗan takara babu wata matsala,” kamar yadda ya bayyawa BBC Hausa.

Da yake Magana kan matsalar tsaro a Najeriya Atiku ya ce rashin zaman lafiya da kasar ke fuskanta abun takaici ne.

‘Babu shakka akwai matsalolin rashin zaman lafiya kuma waɗannan abubuwan sun faru ne don rashin shugabanci’.

A fagen tattalin arziki kuwa Atiku ya ce lamarin ya wargaje kasancewar ɓangare ne da ya shafi dukkan ƴan Najeriya.

Leave a Reply