Kano Ayau Hausa, Siyasa

2023: Kwamishinoni 3 sun sauka daga muƙamansu a Kano

Mukhtar Ishaq Yakasai Kwamishinan Ma’aikatar Ayyuka na Musamman na Jihar Kano, Sanusi Said Kiru, Kwamishinan Ilimi da Ibrahim Ahmad Karaye, Kwamishinan Ma’aikatar Yawon Buɗe-idanu ta Jihar Kano sun ajiye muƙamansu domin yin takara a mataki daban-daban.

A tuna cewa a yau Lahadi ne Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin duk wani mai riƙe da muƙami a gwamnatin sa kuma yake da sha’awar tsaya wa takara to ya ajiye muƙamin kafin gobe Litinin.

Daily Nigerian Hausa ta rawato cewa, fitar sanarwar ke da wuya, sai a ke ta samun kwamishinoni na ajiye ayyukan su.

Tuni dai Kwamishinoni uku, da suka haɗa da Murtala Suke Garo, Musa Iliasu Kwankwaso da Nura Muhammad Dankadai su ka sanar da ajiye muƙamansu.

Shima Muntari Ishaq ya ajiye mukaminsa ne sabo da zai tsaya takarar Majalisar Tarayya mai Wakiltar Karamar Hukumar Birni, yayin da shi kuma Ibrahim Ahmad zai yi takarar Majalisar Tarayya a Kananan Hukumomin Karaye da rogo.

Shima Sanusi Kiru ya ajiye aiki ne saboda zai yi takarar Majalisar Wakilai ta Taraiya a mazaɓar Kiru/Bebeji.

Yanzu haka dai Kwamishinoni 6 kenan su ka ajiye muƙamansu a wannan rana sakamakon umarnin da Gwamna Ganduje ya bayar a daren jiya.

Leave a Reply