Siyasa

2019: Wadanda za su fafata a zaben gwamnoni

A ranar Asabar da Lahadi da suka gabata ne, manyan jam’iyyun siyasar kasar nan APC da PDP suka fara gudanar da zaben fid-da-gwani na ’yan takarar gwamnonin jihohi a zaben da zai gudana a badi.

Duk da cewa an dage zabubbukan a wasu jihohi, ’ya’yan jam’iyyun a wasu jihohi sun gudanar da zaben fitar da gwanin inda suka fitar da wadanda za su rike musu tuta don fafatawa a zaben gwamnonin.

Jihar da ta fi kowace shiga tsaka-mai-wuya ga Jam’iyyar APC mai mulki wajen zaben fitar da gwani a kasar nan ita ce Jihar Legas, inda sakamakon kai-ruwa-rana a tsakanin Jagoran Jam’iyyar APC na Kasa kuma Uban siyasar Jihar Sanata Bola Tinubu da Gwamnan Jihar Akinwumi Ambode, jam’iyyar ta botsare wa Gwamnan inda ta tsayar da wani dan takara na daban. Gwamnan Ambode wanda ya nuna turjiya don tsaya takarar a karshe ya saduda ya mika wuya, inda ya amince da zaben fitar da gwani na APC, wanda ya bayar da gagarumar nasara ga abokin karawarsa Babajide Sanwo-Olu.

A shekaranjiya Laraba Gwamna Ambode ya bayar da kai bori ya hau inda ya yi jawabi na musamman ga al’ummar jihar ta kafafen watsa labarai yana amincewa da zaben fitar da gwanin tare da taya Babajide Sanwo-Olu murna.

Gwamna Ambode ya ce, “Wannan zabe na fid da gwani muhinmmin abu ne da ya dauki hankalin al’ummar kasa baki daya, an yi shi kuma an gama, ba zan bari wannan abu ya kawo tarnaki ga muhinmman ayyukan da muka dauko ba, zan tabbatar na cika aikina, na kuma mika mulki a karshen wa’adin mulkina yadda ya kamata. Ina kira ga daukacin magoya bayana su goya wa Jide Sanwo-Olu baya, za mu ci gaba da aiki tare domin cimma kyawawan manufofin jam’iyyar mu ta APC.”

Jama’a da dama sun yi mamakin yadda Gwamna Ambode ya rungumi kaddara, bayan a baya ya soki Jide da kausasan kalamai ya ce ba zai iya jan ragamar Jihar Legas ba, saboda ba ya da kwarewa kuma ya taba haduwa da tabin hankali.

A Jihar Filato, Gwamna Simon Bako Lalon ne APC ta tsayar takara ta hanyar tabbatarwa saboda rashin abokin takara, kuma zai fafata ne da babban mai kalubalantarsa na PDP, Sanata Jaremiah Usaini da ’yan takarar da suka fito daga sauran jam’iyyu.

Sai Jihar Kaduna, inda Gwamna Nasir El-Rufa’i ya lashe zaben fitar da gwanin da kuri’a 2,427 daga cikin 2,457 da wakilan jam’iyyar suka kada.

Gwamnan zai fuskanci babban abokin fafatawarsa Alhaji Isa Ashiru na PDP wanda ya lashe zaben fitar da gwani na jam’iyyarsa da kuri’a 1,330 bayan ya doke ’yan takara 8 da suka hada da Sanata Suleiman Hunkuyi, wanda ya samu kuri’a 564 sai Mohammed Sani Sidi mai kuri’a 560 da tsohon Gwamnan Jihar Mukhtar Ramalan Yero, wanda ya samu kuri’a 36 sai kuma Shu’aibu Idris Mikati mai kuri’a 16, yayin da Jonathan Kish Adamu ya samu kuri’a 2.

A Jihar Bauchi, Gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar ne ya lashe zaben fid da gwani na Jam’iyyar APC da kuri’a dubu 75 da 86, inda ya doke Sanata Ibrahim Yakubu Lame mai kuri’a 3,988 da Dokta Ali Pate mai kuri’a 2,886 da Kyaftin Bala Jibrin mai kuri’a 2,593, kamar yadda shugaban kwamitin zaben Farfesa Ahmad Bakori Muhammad ya sanar a Bauchi.

Gwamna Abubakar zai fafata da babban mai kalubalantarsa Sanata Bala Mohammed na Jam’iyyar PDP da sauran jam’iyyu.

Daga Jihar Taraba, tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Abubakar Sani Danladi ne zai rike wa Jam’iyyar APC tuta a zaben 2019. Tsohon Mukaddashin Gwamnan ya lashe zaben fid-da-gwanin ne bayan ya samu kuri’a dubu 60 da 629, yayin da Farfesa Sani Yahya ya samu kuri’a 7,299, sai Bobboi Kaigama mai kuri’a 5,530 da Aliyu Umar mai kuri’a 4,638.

Sani Danladi zai kara da Gwamna Darius Ishaku na Jam’iyyar PDP da kuma A’isha Jummai Alhassan wanda za ta tsaya takarar Gwamnan a UDP bayan ta bar APC a makon jiya.

A Jihar Oyo, wani tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Adebayo Adelabu ne zai rike wa APC tuta a zaben na badi. Adelabu jikan fitaccen dan siyasar nan na Ibadan ne Adegoke Adelabu,wanda aka fi sani da  Penkelemesi.

A Jihar Nasarawa kuwa Injiniya Abdullhai Sule ne zai ja linzamin Jam’iyyar APC don yi mata takara a zaben bayan ya kada abokan takararsa a zaben fid-da-gwani. Shugaban Kwamitin Zaben, Alhaji Abdullahi Adamu Candido ya ce, Injiniya Sule ne ya samu kuri’a 926, inda ya doke Alhaji Aliyu Wadada wanda ya samu kuri’a 519 da Mataimakin Gwamnan Jihar Mista Silas Ali Agara mai kuri’a 356 da Danladi Enboluaza mai kuri’a 246 Ja’afaru Muhammed mai kuri’a 105 da Alhaji Zakari Ede mai kuri’a 88.

Abdullahi Sule zai fafata da dan Majalisar Wakilai Dabid Umbugadu na Jam’iyyar PDP da tsohon Ministan Labarai, Labaran Maku na Jam’iyyar APGA.

A Jihar Neja Gwamna Abubakar Sani Bello ne zai rike wa APC tuta inda zai sake fafatawa da babban abokin karawarsa Umar Nasko na Jam’iyyar PDP, wanda ya kayar da masu son tsayawa takara su hudu a PDP da suka hada da tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar, Musa Ibeto.

Jam’iyyar APC a Jihar kebbi ta kara bai wa Gwamna Abubakar Atiku Bagudu damar sake tsayawa takarar a zaben badi bayan da wakilan jam’iyyar 3,318 suka zabe shi a zaben fid-da-gwani.

Gwamna Atiku Bagudu shi kadai ne dan takarar da ya tsaya a zaben da uwar jam’iyyar ta tura Ferfesa Monday Osunber ya jagoranta inda ya shaida wa jama’a cewa Abubakar Atiku ya ci ba hamayya.

Gwamnan Jihar Samuel Ortom ne zai rike wa Jam’iyyar PDP tuta a zaben na badi bayan ya lashe zaben fid-da-gwani da kuri’a 2,210 yayin da mai bi masa John Tondo, ya samu kuri’a 475. Gwamna Ortom zai fafata ne da babban mai kalibalantarsa Emmanuel Jime na Jam’iyyar APC.

Sai dai wani babban abin da yake jan hankali game da zaben fid-da-gwanin shi ne fitar da ’yan takarar Gwamna bibbiyu da aka samu a Jam’iyyar APC a jihohin Kuros Riba inda

Usani Usani da Sanata John Owan kowanne ke bayyana kansa da dan takara. Duk wanda jam’iyyar ta daidaita a kansa zai fafata ne da Gwamna Ben Ayade wanda zai rika wa PDP tuta a zaben na badi.

Sai kuma Delta inda Farfesa Pat Utomi da Great Ogboru kowannensu ke ikirarin yi wa APC takara da kuma Ribas inda Magnus Abe da Tonye Cole kowanensu ke da’awar cewa shi ne halattaccen dan takarar jam’iyyar. Haka lamarin yake a Jihar Imo a tsakanin Mista Uche Nwosu da Sanata Hope Uzodimma. Ita ma Jam’iyyar PDP a Jihar Borno ’yan takara biyu ne suke da’awar halaccin kasancewa ’yan takararta , wato Alhaji Mohammed Imam da Mohammed Wakil. Kuma dayansu zai fafata da Farfesa Mustapha Umara Zulum na Jam’iyyar APC.

 

Waxanda za su fafata a zaven gwamnoni

Leave a Reply