Kano Ayau Hausa, Manyan Labarai

Ɗan bindiga ya harbi mutum biyar a Amurka

Mutum biyar ne suka mutu yayin da wasu guda shida suka jikkata a wani harin bindiga a birnin Louisville da ke jihar Kentucky na Amurka.

Ƴan sanda sun ce harin ya afku ne a wani banki da ke cikin birnin.

A wani taron manema labarai da ƴan sanda suka kira bayan afkuwar lamarin, sun ce an ɗauki mutum shida da suka jikkata, ciki har da wani jami’in tsaro, zuwa asibiti don yi musu magani.

Cikin waɗanda suka rasa rayukansu har da ɗan bindigar da ya kai harin.

An umarci jama’a da su ƙauracewa wajen da lamarin ya faru, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Wani hoton bidiyo da aka ɗauka a yankin, ya nuna jami’an soji kewaye a yankin da aka kai harin.

Leave a Reply