BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Ƴan Sanda sun daƙile harin ‘ƴan bindiga a hanyar Kaduna-Abuja

Ƴan Sanda a Jihar Kaduna sun daƙile wani harin ƴan fashin daji a ƙauyen Kurmin Kare da ke Ƙaramar Hukumar Chikun ranar Lahadi.
Kakakin Rundunar Ƴan Sanda a jihar, ASP Mohammed Jalinge a wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin a Kaduna cewa jami’an ƴan sanda sun kuma ƙwace makamai da alburusai a hannun ƴan ta’addan.
Ya ce ƴan sandan sun daƙile harin ne bayan rundunar ta samu bayanan sirri cewa an ga ƴan fashin daji da dama a yankin ƙauyen Kurmin Kare a kan babban titin Kaduna-Abuja.
Ya ce a sumamen da a ka kai wa ƴan ta’addan, an ƙwato bindiga kirar AK 47 ɗauke da harsashi 10 masu girman 7.62x39mm da alburusai 180 na 7.92x57mm bindiga ƙirar ‘General-Purpose Machine Gun (GPMG).
“Yayin da da yawa daga cikin ‘yan fashin suka tsere da raunukan harbin bindiga, ana ci gaba da kokarin gano wadanda suka jikkata, domin a kama su da kuma gurfanar da su a gaban kuliya,” inji shi kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta kalato daga NAN.
Mista Jalige ya bukaci al’ummomin da ke makwabtaka da su da su kai rahoton duk wanda ya samu raunuka ga jami’an tsaro mafi kusa sannan ya ba da tabbacin cewa za a yi amfani da bayanan da suka samu cikin sirri.

Leave a Reply