BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Zuwa watan Disamba ‘ƴan ta’adda za su zama labari– Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta ce za ta kawar da dukkan ƴan ta’adda daga watan Disamban wannan shekara.

Daily Nigerian Hausa ce ta kalato dag Daily Trust cewa, Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya bayyana a Abuja, yayin wani taron manema labarai na haɗin gwiwa da suka yi da ministocin tsaro, da yaɗa labarai da harkokin ƴan sanda da kuma babban hafsan sojin ƙasa.

’Yan bindiga sun kama barawo, suka mika wa jami’an tsaro a Katsina

Aregbesola ya ce: “Yan Najeriya sun tabbatar mana da cewa an tabbatar da tsaron su. Don haka, mun zo nan don tabbatar muku cewa kuna cikin kariya, shi ya sa muka zo nan daga umarnin shugaban kasa cewa kuna cikin aminci, kuma kowace rana zuwa Disamba, amincinmu zai ƙaru.

“Abin da mu ke fuskanta a yanzu shi ne ɗan fadace-fadace da hare-hare na tsoro daga waɗanda aka fatattake su a wani yanki ko kuma wani motsi don barazana ta ƙarya cewa har yanzu suna da ƙarfi.

” Babban burinmu shi ne mu kawar da su gaba ɗaya, mu maido da cikakken zaman lafiya a kowane inci na kasar Nijeriya; wanda za mu yi da yardar Allah, nan da Disamba na wannan shekara.

“Za a ga kamar ba mai yiwuwa ba ne amma mun kuduri aniyar tabbatar da cewa kowane inci na kasar Najeriya yana da tsaro. Hukuncin yana nan kuma an ba da oda.”

Ya ce kalubalen tsaro na yanzu ya ta’azzara ne ta hanyar kullen COVID-19 duk da matakan da gwamnati ta ɗauka.

“Amma za mu ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya da na kasashen waje da ke tsakiyar mu. Za mu ci gaba da yin aiki don zaman lafiyar al’umma tare da daƙile abubuwan da ke zama barazana ga jama’a.

“Za mu ɗauki cikakken ikon gwamnati don tabbatar da kowane inci na ƙasarmu. Ba za mu huta ba har sai an samu cikakken zaman lafiya a Najeriya,” inji shi.

Leave a Reply