Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya jajantawa ‘yan kungiyar kwadago da ASUU, bisa yadda gwamnatin tarayya ta gaza biya wa kungiyar ASUU bukatunta na kudaden albashi da alawus-alawus har ta kai tsunduma yajin aiki da Ƙungiyar ta ASUU ta shiga.
Yayin wata zanga-zangar lumana da aka gudanar a ranar Talata a birnin Kano, Ganduje ya tabbatar wa kungiyar kwadago ta Najeriya cewa kungiyar gwamnonin Najeriya za ta yi duk mai yiwuwa don ganin an sasanta rikicin da ke tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i.
Legit ta rawaito cewa, Ganduje ya kuma yi alkawarin mika wasikar da ya karba daga shugabannin kwadago zuwa ga ministan ilimi, Adamu Adamu, domin mikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kamar yadda Nasara Radio ta kalato.
Shugaban kungiyar NLC reshen Kano, Kabiru Minjibir, ya ce zanga-zangar na bin umarnin hedikwatar kungiyar ta kasa ne na tilastawa gwamnati yin abin da ya dace. Ya kuma yabawa Ganduje kan rashin daukar wasu abokan aikinsa na hana malaman jami’o’i albashi saboda suna cikin yajin aiki.