BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Zan bar tarihi mai kyau-Buhari

A yau Asabar ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa wadanda suka yi yunkurin kawo wa Najeriya tarnaki a kan zaman lafiya sun sha kashi a fafatawar da suke ti yi, yana mai cewa yanayi ingantacce na jiran Najeriya a 2023 da kuma gaba.

Shugaban ya bayyana hakan ne a sakonsa na Kirsimeti na shekarar 2022 inda ya bayyana bikin a matsayin na musamman.

“Sako na na Kirsimeti ne na ƙarshe a matsayina na shugaba. Makonni ashirin da biyu kenan wannan su ka rage gwamnatin zata mikawa wata.

“Wannan wata dama ce ta nunawa sauran kasashen duniya cewa lallai Nijeriya a shirye take ta tabbatar da tsarin dimokuradiyya kamar yadda ake gani a kasashen duniya.

“Bari zaman lafiya da farin cikin da ke tattare da wannan lokaci ya ci gaba da wanzuwa har zuwa sabuwar shekara har zuwa zaben da za a yi a watan Fabrairu da kuma bayan nan.

“Ina so in tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa masu neman kawo cikas ga zaman lafiyar al’ummarmu sun yi rashin nasara a yakin.

“Kasarmu na da albarkar arzikin dan Adam da abin duniya. Mu yi murna da albarkar mu a wannan lokaci tare da amincewa cewa kyakkyawan yanayi na nan na jiran Nijeriya ,” inji shi kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta fassaro.

Leave a Reply