Kano Ayau Hausa, Siyasa

Zaben Kano zai zama mizanin auna adalcin INEC – Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya ce zaben gwamna da za a kammala a jihar Kano zai tabbatar ko kuma rushe darajar gwamnati da hukumar zaben kasar INEC.

Kano na daga cikin jihohi biyar da hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta ce za ta gudanar da zaben cike gibi a cikinu, a ranar 23 ga watan Maris.

Wannan mataki ya zo ne bayan da hukumar ta INEC ta ce zabukan jihohin ba su kammala ba saboda soke sakamakon wasu mazabu, wadanda yawan kuri’unsu suka zarce tazarar da ke tsakanin ‘yan takara biyu mafiya yawan kuri’u a zaben na gwamna.

A tattaunawar sa da BBC gabanin zaben, sanata Rabiu Kwankwaso ya ce zaben na jihar Kano na daukan hankulan al’ummar Najeriya da ma wadansu kasashe.

Ya kara da cewa ‘wannan shi zai tabbatar da darajar ita kanta hukumar zabe da gwamnati, ko kuma ya ruguje ta.’

A zaben gwamna da aka gudanar na jihar Kano, ranar 9 ga watan Maris, jam’iyyar PDP ce ke kan gaba da yawan kuri’a, inda ta samu kuri’u 1,014,343, sai jam’iyyar APC mai mulkin jihar wadda ta samu kuri’a 987,829.

Sauran jihohin da za a kammala zabukan gwamna a cikin su su ne Sokoto, da Benue, da Adamawa, da kuma Filato.

Leave a Reply