Amurka ta yi babban gargadi ga bangarorin siyasa a Najeriya kan makomar zaben kasar na 2019.
Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar a shafinta na twitter, ta ce dole ne jami’an tsaron Najeriya su tabbatar da zaman lafiya domin al’ummar kasar su samu damar ‘yancisu.
Ta kuma yi kira ga bangarorin siyasa a Najeriya, musamman hukumar zabe da su tabbata zabukan da za a yi a mako mai zuwa ya kasance an tsaftace shi daga dukkan wata matsin lamba daga gwamnati ko barazana daga kasashen waje
Sanarwar ta ambato sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo na cewa “dole ne a kama wadanda suka yi katsalandan a harkokin zabe ko kuma suka tayar da husuma da alhakin yin hakan.”
Ya ce zaben 2019 dama ce ga Najeriya da ta karfafa matsayinta na shugabar demokradiyya a nahiyar Afirka.
Mista Pompeo ya ce “Amurka na goyon bayan sahihin zabe wanda za a yi cikin kwanciyar hankali, wanda kuma zai cika burin al’ummar Najeriya.” kamar yadda BBC ta rawaito
Sai dai, mai bayar da shawara kan harkokin tsaron Najeriya, Mohammed Monguno ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa ba za yi amfani da jami’an tsaro wajen cimma wata manufa ta daban ba a lokacin zaben mai zuwa.
Monguno ya bayyana haka ne a wani taron masu ruwa da tsaki kan zaben 2019 a Hukumar Zaben mai zaman kanta, INEC a Abuja.