Kano Ayau Hausa, Labarai

Za mu kawo karshen ‘yan bindiga da zarar PDP ta dawo mulki-Wike

Gwamnan Jihar Ribas kuma mai neman tikitin shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Nyesome Wike, ya ce hanya mafi sauki na kawo karshen ‘yan bindiga dadi a Nijeriya shi ne yin umumu wajen korar APC daga mulki tare da maye gurbinta da jam’iyyar PDP. 

Wike wanda ya bayyana hakan a garin Jos babban birnin jihar Filato sa’ilin da ke ganawa da wakilan jam’iyyar PDP na kasa daga jihar ta Filato.

Ya ce: “Yan bindiga ba su mamayi Nijeriya ba har sai lokacin da APC ta dale kan mulki. Jam’iyyar ita ce ta haifi ‘yan bindiga tun lokacin da ta zo mulki kuma tun daga wannan lokacin babu zaman lafiya.

“Zallar aikin da APC ta kawo jihar Filato shi ne ‘yan bindiga da kashe-kashe. Abun da kawai kake ji daga jihar Filato a kullum rana shi ne an kashe mutum 10, 20, 30, ko mutum 100 abun takaici kuma ba abun lamunta ba ne hakan.”

Ya jawo hankalin al’ummar jihar da su bada hadin kai wajen tabbatar da PDP ta amshi mulki a 2023 domin ceto jihar da ma kasa baki daya daga halin kunci da ake cikin a yau.

Gwamnan Wike ya kuma shaida wa wakilan jam’iyyar da cewa ya kasance a Jos ne domin bayyana musu aniyarsa ta neman shugabancin Nijeriya, yana mai fadin shine mutumin da ya dace da tunkarar kalubalen da suke jibge a Nijeriya da gyara irin barnar da APC ta yi da zarar ya samu damar hakan. Sai ya nemi su mara masa baya domin cimma wannan manufar da ya sanya a gaba, kamar yadda Leadership Hausa ta kalato.

Tun da farko a jawabinsa, Shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Hon. Chris Adukuchili Hassan, ya ce Wike ya jima da zama aboki kuma aminin jihar Filato na tsawon lokaci.

Ya ce wakilan jihar za su yi la’akari da Wike, ya ce lokaci ne ya yi da za su saka masa bisa nasa kokarin.

Leave a Reply