Kano Ayau Hausa, Labarai

Za mu bincika zare kudin fansho da Gwamna Ganduje ya rika yi

Wata sabuwar batarnaƙa ta kunko kai a Kano, yayin da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir-Yusif ya sha alwashin ƙwato kuɗaɗen fansho N5.4bn da gwamnatin tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ba ta biya ba, amma kuma ta fitar da kuɗaɗen.

Gwamna Abba Kabir-Yusuf na Jihar Kano ya ce a shirye ya ke ya yi amfani da duk wata hanya ta doka wajen karɓo kuɗaɗen fansho da Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta ke cirewa duk wata daga albashin ma’aikata da suka kai sama da Naira biliyan 5 kuma ba a sanya su a asusun gwamnati ba.

Gwamnan ya ce ba za a amince da wani ya cire kuɗaɗen fansho na ma’aikata duk wata ba, kuma ba tare da an tura kuɗaɗen ba.

Da yake Jawabi a lokacin bikin bayar da garatuti Naira biliyan 5 ga ma’aikata 4,000 da suka yi ritaya, Gwamna Abba ya lura cewa biyan fansho ba gata ba ne ga ma’aikata face haƙƙin su ne da ya wajaba a biya su.

Gwamnan ya buƙaci ‘yan fanshon da su rubuta takardar koke ga Gwamnatin Jihar Kano, domin a binciki yadda ake cire musu kuɗaɗen fansho duk wata.

Ya ba da tabbacin cewa gwamnatin sa za ta tabbatar an ƙwato musu kuɗaɗen su.

Ya ci gaba da cewa, “abbatarwar da muke muku yanzu ita ce, duk kuɗaɗen da aka cire daga cikin kuɗaɗen fansho a duk wata da suka haura Naira biliyan 5 ba a tura su a baitul malin gwamnati ba, sai dai muna zargin an kai su a wani asusu na sirri ne, amma mun ƙudiri aniyar ƙwato su ta hanyar doka”, gwamnan ya tabbatar da haka.

Gwamna Abba ya ƙara da cewa gwamnatin sa ta gaji bashin Naira biliyan 43 na fansho daga gwamnatin Ganduje.

Abdulkadir Abdussalam Babban Akanta Janar na Jihar Kano, ya bayyana cewa Gwamna Yusuf ya ƙudiri aniyar biyan kuɗaɗen fansho na shekaru goma.

Shugaban Kungiyar ’Yan fansho ta Najeriya reshen Jihar Kano, Kwamared Salisu Gwale ya bayyana cewa kafin zaɓen 2023, “mun tambayi yadda sabuwar gwamnati za ta magance matsalar ‘yan fansho a Kano da sama da Naira biliyan 43 da ba a biya ba.

Salisu Gwale ya nuna baƙin cikin sa kan yadda gwamnatin Ganduje ta yiwa harkar fansho riƙon sakainar kashi.

Leave a Reply