BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Yau za a yanke wa Ekweremadu hukunci a Birtaniya

A yau ne kotun hukunta manyan laifuka ta Old Bailey da ke Birtaniya za ta yanke wa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa ​​Beatrice Ekweremadu da wani likita hukunci, kamar yadda BBC ta kalato.

Wannan ya biyo bayan samun ɗan majalisar dattijan da matarsa da laifin yunkurin safarar sassan ɗan adam a watan Maris.

Kotun ta kuma sami wani likita mai shekaru 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da ɗan siyasar wajen samo mutumin saboda a cire masa koda, inda ake sa ran yanke musu hukunci a karon farko a irin dokokin bauta ta zamani.

Matashin da aka so amfani da ƙodar tasa, wani mai ƙaramar sana’a ne a birnin Legas.

An kai shi Birtaniya ne a bara domin gudanar da aiki a asibitin Royal Free Hospital da ke biornin London.

Ya ce an yi alƙawarin samar masa aiki a Birtaniya saboda taimakon da zai yi, sai dai ya ce ya gane cewa ana masa shigo-shigo ba zurfi ne bayan tattaunawa da likitoci a ƙasar ta Birtaniya.

Leave a Reply