Big Story, Latest News

Yau dokar takaita cire kudi na CBN za ta fara aiki

A yau Litinin dokar takaita kudi ta ATM da babban bankin kasa wato CBN ya fitar ke soma aiki a fadin Najeriya.

CBN ya ce a yanzu ɗaiɗaikun mutane za su iya cire kudi har naira 500,000 yayin da kamfanoni kuma za su iya cire naira miliyan biyar duk mako.

Idan mutum na son cire kuɗin da ya fi wannan adadi yawa to sai an caje shi kashi biyar cikin 100 ga mutum da kashi 10 cikin 100 ga kamfani na yawan kudin da zai cire.

Sannan bankin ya umarci bankuna su daina loda tsoffin takardun naira da aka sauya a nau’rorin ATM, inda suka bukaci kowanne banki ya ke fitar da sabbin kudade.

Leave a Reply