GAJERAN LABARI, Kano Ayau Hausa

Yan ta’adda sun kashe ‘yan sandan da suka kubutar da mahajjatan Sokoto

Mahukuntan jihar Sokoto a Najeriya sun tabbatar da mutuwar jama’an ‘yan sanda 6 da suka fafata da ‘yan ta’addan da suka yi yunkurin yin garkuwa da maniyyata aikin hajjin Karamar Hukumar Isa ta jihar.
Yanzu haka gawawwakin ‘yan sandan na nan ajiye a Assibitin Koyarwa ta Jami’ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto.
Wadanda lamarin ya faru a kkan idonsu sun tabbatar wa RFI Hausa cewa, lallai an yi artabu tsakanin da ‘yan ta’addan da Jami’an yan sanda masu rakiyar maniyyata aikin hajjin.
Bayanai na cewa, daukacin maniyyatan sun kubuta daga fadawa tarkon garkuwar ‘yan bindingar kuma wani lokaci a yau ne ake sa ran jirginsu zai tashi domin kama hanyar zuwa kasar Saudiya don sauke farali.
Karamar Hukumar Isa ta jihar Sokoto na da maniyyata aikin hajjin bana 21.

Leave a Reply