Al’ajabi, Kano Ayau Hausa

‘Yan ta’adda sun kashe sojoji 11 a Kaduna

Akalla sojoji 11 ne aka kashe bayan wasu ‘yan ta’adda sun kai farmaki a sansanin sojojin Najeriya da ke kauyen Polwire a karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.
Wata majiya da ta bayyana hakan ga SaharaReporters ta ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin.
Ya ce ‘yan bindigar sun zo da yawa ne a kan babura inda suka yi artabu da sojojin da aka shafe sa’o’i biyu ana gwabzawa kafin su fatattake su.
Haka kuma an kashe ‘yan kungiyar ‘yan Bijilante ta Kaduna guda uku a yayin harin.
A ranar Litinin din da ta gabata, SaharaReporters ta ruwaito cewa ‘yan ta’addan sun kuma kai farmaki kauyukan da ke kananan hukumomin Kagarko da Kachia a jihar Kaduna.
Sun kashe mutane akalla 17 a cikin kauyukan hudu bayan sun yi garkuwa da wasu 22 a kusa da Angwar Ma’aji a Jere, karamar hukumar Kagarko.
Hakan ya faru ne sa’o’i 24 da sufeto Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, ya ziyarci babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Jere, wanda ke da iyaka da Tafa-Sabon-Wuse a Jihar Neja, yana kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Wani mazaunin Angwar Maji, Shehu Bala, wanda ya tabbatar da sabbin hare-haren, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na daren Lahadi.
Ya ce ‘yan bindigar da suka zo da yawa sun mamaye wasu gidaje inda suka yi awon gaba da mutane 22 ciki har da mata biyar.

Leave a Reply