BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

‘Yan bindiga sun sace mata sama da 30 a Zamfara

Wasu ƴan bindiga sun kai hari wasu ƙauyukan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, inda suka kashe mutane da dama tare da sace ƴan mata fiye da 30 a ƙaramar hukumar Maradun.

Maharan sun abka ƙauyukan Sakkiɗa da Janbako a ranar Asabar da rana inda suka kashe mutum sama da 20 a Sakkiɗa tare da jikkata karin wasu.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewa, an dauki ƴan mata fiye da 30 a kauyen Gora a yayin da suka tafi yin itace a dajin Ɗaggera.

Ya ce, “ƴan bindigar sun bayar da sanarwa tun kafin sace yaran cewa idan har muna so mu yi noma a Ɗaggera a bana, to sai mun zauna mun yi sulhu da su, kuma mu yi ta sulhu da su amma bamu san dalilin sace mana yaran ba.”

Shima wani mazaunin Janbako, ya shaida wa BBC cewa, suna zaman lafiya sai ga sanarwa ta zo daga kauyen da ke kusa dasu wato Sakkiɗa cewa barayi sun shiga suna so akai musu dauki.

Ya ce,” Ba tare da bata lokaci ba, mutanen kauyenmu da ‘yan sa kai suka dauki makamai aka tunkari garin, suna isa garin ashe barayin dajin sun yi musu kwanton bauna, nan suka bude musu wuta aka kuma kashe mutane, don mu a garinmu an yi jana’izar mutane sun kai 22.”

Mutumin ya ce, an kira jami’an tsaro amma suka ce ba zasu samu damar zuwa ba a daidai lokacin saboda motarsu ta yaki da suke amfani da ita bata nan.

Ya ce, daga bisani bayan jami’an tsaron sun zo sun bi barayin amma sai suka dawo da Babura biyu kawai na barayin.

“ Akwai mutane da dama da suka jikkata, kuma mu a Janbako, babu wani jami’in tsaro da ke kwana damu ko yake zaune a garin.”

Rundunar ƴan sandan Najeriya a jihar ta Zamfara ta tabbatar wa BBC kai harin amma ta ce bata da karin bayani tukunna.

Jihar Zamfara dai na daya daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da hare haren ‘yan bindiga da satar mutane don neman kudin fansa.

Kazalika hare haren ‘yan bindiga kan tilastawa mazauna yankunan jihar zama ba tare da noma gonakinsu ba, abin da mazauna yankunan ke kokawa akai ke nan kullum.

A ko da yaushe mutanen dai su na neman daukin gwamnati a kan wannan matsalar.

Leave a Reply