Bayanan da ke fitowa daga Jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya sun nuna cewa an kashe mutum 135 yayin wasu hare-hare da ‘yan bindiga suka kai a wasu ƙauyuka ranar Lahadi.
Maharan sun far wa a aƙalla ƙauyuka hudu da ke Ƙaramar Hukumar Kanam a kan babura, inda suka dinga harbe mutane tare da ƙona gidaje masu ɗumbin yawa da kuma sace shanu.
Hukumomi ba su yi cikakken bayuani game da hare-haren ba.
Sai dai wani basaraken gargajiya a yankin ya shaida wa BBC cewa tuni aka gano gawar mutum 54 a kauyen Kukawa da kuma gawar mutum 34 a kauyen Gyambau.