BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

‘Yan bindiga sun kashe mutum 6 tare da garkuwa da wani sarki a Jihar Kano

A daren jiya yan bindiga sun shigo garin ƙarfi dake ƙaramar hukumar Takai a Jihar Kano inda suka kashe mutane 6, suka raunata 2 sannan suka tafi da Sarkin garin.

Wani mazaunin garin a zantawar mu da shi ya bayyana cewa yan bindigar sun shigo ne da karfe 12 saura na dare suna harbe-harbe da bindiga.

”Wajen 12 shaura na dare yan bindiga sun shigo Karfi dake Takai LG suna harbe-harbe, mutane ma sun dauka masu babura ne suke wasa, sai ganin su akai akan babura sun zo gidan Sarkin Ƙarfi suka dauke shi suka tafi dashi,” kamar yadda muka nado daga shafin Aliyu Samba a Facebook.

Ya sheda mana cewa yan bindigar sun shigo ne daga bangaren kudancin garin inda sukai iyaka da jihar Bauchi, sun harbi mutane 8 a hanyar komawar su bayan sun yi garkuwa da Sarkin.

Shida daga cikin wadanda aka harba sun riga mu gidan gaskiya, yayin da ragowar mutum 2 suke kwance asibiti. A halin yanzu ana shirye-shiryen yin Jana’izar wadanda suka rasu a garin na karfi.

Leave a Reply