BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Yan bindiga sun kashe hazikin ‘yan sanda a Katsina

Rahoton DW Hausa ya bayyana cewa, mahara sun kashe babban kwamandan ‘yan sanda a yankin Dutsinma da ke Katsina, ACP Aminu UMar.

Sanarwar da rundunar ‘yan sanda reshen jihar ta fitar ta ce ACP Aminu ya rasa ransa tare da wani dan sanda guda daya bayan wata arangama da suka yi da barayi a dajin Zakkah da ke cikin karamar hukumar Safana.

Kafin sadaukarwar da ACP Aminu ya yi a ranar Litinin da daddare ya kasance jajirtaccen dan sanda; mara tsoro, a cewar abokan aikinsa.

Leave a Reply