Mahara a kan babura sun far wa shingen binciken jami’an kwastam da ke Mil Takwas, wanda ba nisa sosai da shiga garin Katsina, inda suka ƙona motoci hudu.
Lamarin ya faru karfe 12 na dare ranar Lahadi. Wani da bai yadda a faɗi sunan shi ba ya tabbatar da cewa an kashe direban motar fasinja a daidai wurin, amma ba su san yadda aka yi da fasinja da ke ciki ba.
Mai magana da yawun hukumar kwastam a Jihar Katsina Isah Danbaba ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, inda ya ce ƴan bindigan sun kai harin ne kan babura sama da 200.
Ya kara da cewa tun da farko jami’an su sun samu bayanan sirri game da harin, kuma ganin cewa maharan na da yawa shiyasa suka yi gudun tsira da ran su.
Kuma duka ma’aikata 12 da ke shingen babu wanda ya samu rauni.
Majiyar ta kuma ce maharan sun shiga kauyen Zamfarawa inda suka kashe mutum takwas.
A kauyen Walawa kuwa sun tafi da mata da dama wadanda ba su iya tserewa ba