Kotun Masana’antu ta Ƙasa ta ɗage shari’ar da ke tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, zuwa ranar 16 ga watan Satumba.
Mai shari’a Polycap Hamman ta ɗage shari’ar don baiwa ɓangarorin biyu damar shigar da takardun da su ka dace na ƙarar.
Shugaban yaɗa labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar kwadago da samar da aikin yi, Olajide Oshundun, ya bayyana cewa ministan kwadago da samar da ayyuka Chris Ngige ne ya miƙa batun ga magatakardar kotunan masana’antu ta kasa, inda ya ƙara da cewa daga nan ne gwamnati ta garzaya kotu.
Ya ce ma’aikatar ta kuma roƙi kotun da ta baiwa ASUU umarnin janye yajin aiki, yayin da ake kokarin shawo kan rikicin, kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta kalato.
A tuna cewa ASUU ta shiga yajin aikin ne tun watan Fabrairun bana wanda ya kai ga rufe jami’o’in gwamnati na tsawon watanni takwas.