FITATTUN MATA, Kano Ayau Hausa

Yadda na mallaki filin da za a rusa-Muhuyi

Shugaban hukumar yaƙi da rashawa da karɓar koke-koken al’umma ta jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya tabbatar da cewa gwamnatin da ta gabata ta bashi fili akan titin zuwa tsohuwar jami’ar Bayero dake Kano, kuma ya siyar dashi a lokacin da yake bukatar kuɗi, kuma an tabbatar masa wuri da bai saɓa ƙa’ida ba.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, daya daga cikin mamallakan gine-ginen da ke hanyar BUK, Isma’ila Bello, yayi korafin cewa, shugaban hukumar yaƙi da rashawar ne ya siyar masa da filin, wanda a halin yanzu yana cikin gwamnati mai ci.

Dan kasuwar ya kuma zargi gwamnatin da nuna rashin adalci a shirin rusau da take yi na baya-bayan nan, inda yace wasu daga cikin gine-ginen da aka sanya cikin wadanda za a rusa an same su ne bisa ka’ida daga wuraren mutanen da ke da alaka da gwamnati mai ci.

A ranar juma’a ne dai hukumar tsara birane ta jihar Kano (KNUPDA) ta sanya jan fenti a wasu gine-gine dake kan titin zuwa tsohuwar jami’ar Bayero, wanda ke gaban Ganuwar Kano mai tsohon tarihi a ƙasar Hausa, kamar yadda Nasara Radio ta ruwaito.

Leave a Reply