Al’ajabi, Kano Ayau Hausa

Yadda jarirai ke ‘murmushi’ idan mai juna-biyu ta ci karas

Masana kimiyya sun gano cewa ‘yan tayin da ke cikin mahaifa, na yin murmushi idan iyayensu suka ci karas, haka kuma suna yin fushi idan iyayen suka ci ganye dangin salak.

Cibiyar binciken ‘yan tayi ta jami’ar Durham da ke Birtaniya, ta ce binciken shi ne irinsa na farko da ya samu hujjar da aka nada ta na’urar daukar hoton ciki da ke nuna yadda ‘yan tayin ke kasancewa lokacin da iyayensu ke cin abinci iri-iri.

An gudanar da binciken ne a kan mata masu juna-biyu fiye da 100 tare da jariran da ke cikinsu a Ingila.

An bai wa mata masu juna 35 kwayoyin da ke dauke da sinadarin karas, sai kuma 34 da aka bai wa kwayoyin da ke dauke da sinadarin ganyen salak, a yayin da aka bar mata 30 ba tare da ba su komai ba.

An nuna yanayin da ‘yan tayin ke ciki ta hanyar na’urar daukar hoton ciki ta 4D

Masu binciken sun wallafa rahotonsu a mujallar kimiyya cewa minti 20 bayan da iyayen suka hadiyi kwayoyin, wata na’urar daukar hoton ciki mai suna 4D ta nuna yadda ‘yan tayin – da ke cikin mahaifa da aka bai wa iyayensu kwayoyin da ke dauke da sinadarin ganye – na murtuke fuska (alamar rashin jin dadi).

Haka kuma na’urar ta nuna yadda ‘yan tayin ke murmushi bayan da aka bai wa iyensu kwayoyin da ke dauke da sinadarin karas.

Su kuma matan da ba a bai wa komai ba jariran da ke cikinsu babu abin da suka yi.

Binciken da suka gabata sun nuna cewa abincin dan adam yana farawa ne tun kafin a haife shi, sakamakon ganowa da aka yi cewa ruwan da ke gudana a jikin ‘yan tayin na dauke da sinadaran abinci daban-daban, ya danganta da irin abincin da iyayensu ke ciki.

To amma wannan sabon binciken na Jami’ar Durham ya ce shi ne bincike na farko da aka nuna yadda ‘yan tayin ke yi bayan cin abinci daban-daban da iyayensu suka yi.

Yaushe dan tayi zai fara jin dandanon abinci?

”Mun sani daga binciken da suka gabata cewa abincin da iyayen ‘yan tayi ke ci, na da matukar muhimmanci wajen lafiyar su bayan an haife su.

To amma abin da ba mu sani ba shi ne yaushe wannan yake farawa,” in in ji Nadja Reissland, daya daga cikin wadanda suka wallafa binciken, kuma shugabar cibiyar binciken ‘yan tayi ta Jami’ar Durham.

Ta shaida wa BBC cewa ‘yan tayi na fara jin alamar sinadarin siga a cikin mahaifa tun a mako na 14.

“A binciken da muka yi, mun bai wa masu juna-biyu kwayoyi a lokacin da cikinsu ke mako na 32 da 36.

“Muna son ci gaba da bincikenmu tare da nadar bayanan wadannan ‘yan tayin bayan an haife su, sannan mu lura ko za su ci gaba da yin murmushi saboda karas, ko nuna fushi saboda ganye dangin salak, kamar yadda suka nuna a lokacin da suke cikin mahaifa.

Me wannan binciken ke kokarin nuna mana dangane da jin dandano ga jarirai?

Reissland ta ce binciken na nuna jarirai suna fara jin dandano tun da wuri, ya danganta da irin nau’in abincin muhallin da suke.

”Idan dan tayi ya ji wani dandanon abinci tun a cikin mahaifiyarsa, to bayan haihuwarsa idan aka ci gaba da ba shi irin wannan abinci, zai ci gaba da cinsa.”

Dandanon daci na kunshe da guba

Ta kuma bayyana wasu dalilan da ke nuna cewa ‘yan tayi na kin dandanon daci.

”Mun kuma gano cewa daci na kunshe da hatsari, kuma ‘yan tayin ba so son dandanon”

To amma tunda ba kowanne dandanon daci ne ke dauke da guba ba, ya kamata mu ilimantar da kanmu da ‘ya’yanmu, mu fahimci cewa, wasu abincin da ke dauke da dandanon daci na matukar taimakawa lafiyarmu.

”Murmushi tare da fushin da aka gani tare da ji a na’urar daukar hoton cikin ”ka iya zama motsin tsoka, wanda motsawa sakamakon dacin” in ji Reissland

Me sauran masana kimiyya ke tunani?

Dakta Daniel Robinson, masanin kimiyyar ‘yan tayi a jami’ar harhada magunguna ta Feinberg a Amurka ya shaida wa kafar yada labarai ta NBC cewa bai kamata mutane su fassara hotunan da na’urar ta dauka ba, wadnda ke nuna ‘yan tayi na bayyana murmshi tare da fushi.

Jaridan Guardian ta ruwaito Dakta Julie Mennella, daga cibiyar binciken sinadarai ta Philadelphia da ke Monell, na cewa binciken ya goyi bayan binciken da suka gabata da ke cewa ‘ya’ya na koyon cin abubuwa daga iyayensu, ta hanyar sinadarin da ake narkarwa daga abincin da iyayen nasu ke ci domin amfanin ‘yan tayin a cikin mahaifa.

Cin abubuwa daban-daban

Beyza Ustun, wanda ya jagoranci binciken ya ce, “bincike da dama sun nuna cewa ‘yan tayi na jin dandano tare da shakar kamshi tun a cikin mahaifa.”

To amma suna dogara ne da sakamakon da ake samu bayan haihuwar jariran, amma wannan sabon binciken namu shi ne na farko da ya samu sakamako tun kafin haihuwa.

“Muna tunanin cewa sakamakon yadda ‘yan tayin ke bayyana yadda suke ji sakamakon sinadari da dama kafin haihuwa zai taimaka wajen sanin abincin da ya kamata a bai wa jariri bayan haihuwarsa.”

Don haka a iya cewa wannan bincike zai taimaka wajen bai wa iyaye haske kan abincin da ya kamata su dora jariransu a kai bayan haihuwasu.

Leave a Reply