Big Story, Kano Ayau Hausa

Yadda bude wajen shakawatar Rahama Sadau ya tayar da kura

A makon jiya ne Jaruma Rahama Sadau ta yi bikin bude katafaren wajen shakawarta mai suna Sadau Home.

Daga cikin abubuwan da a rika gudana a wajen akwai bangaren aski, da gyaran gashi da cin abinci da wasanni da wajen shan shisha.

A taron bude wajen, an nuno Rahama Sadau sanye da doguwar riga ja, wadda ke nuna wani shashen jikinta, lamarin da ya jawo cece-kuce, inda wasu suke ganin hakam bai kamata ba musamman ganin cewa ita musulma ce, kuma mai wakiltar musulmai da Hauwa.

An yi cece-kuce a kan lamarin, inda ita ma Rahama Sadau ta rika mayar da martani ga wadanda suke mata magana, wadanda a ganinta maganar ba su mata dadi ba.

Leave a Reply