Hukumar alhazai ta Najeriya, NAHCON ta bayyana damuwa a kan kutsen da alhazan bogi suka yi a Mina da Arafa wanda ya janyo rashin isassun tantuna a tsakanin mahajjatan Najeriya.
Shugaban Hukumar, Alhaji Zikrullah Hassan ne ya bayyana haka yayin wata ziyarar aiki da ya kai wa Mutawif, kamfanin kula da alhazan ƙasashen Afirka da waɗanda ba Larabawa ba, a birnin Makkah na kasar Saudiyya.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ambato Zikrullah Hassan na cewa “Da farko, zan so na mayar da martani a kan yadda alhazan bogi suka mamaye yankunan aikin Hajjin bana kuma wannan abin kunya ne.
Rashin kudi yana karya farashin fetur a Najeriya
“Ban san iyakar adadinsu ba, amma mun ga mutanen da ba su da wani aiki a Mina, bayan ‘yan kwanaki sai kuma suka mayar da Mina tamkar kasuwa ko kuma wurin biki.
“Duk da haka, ba mu da ikon bincikar su. Ba mu ne ke da ikon tsaro ba saboda haka babu yadda za mu iya tunkarar lamarin, gaskiya hakan abin kunya ne,” kamar yadda BBC ta ruwaito.
Hassan ya ce tantunan da aka yi amfani da su a aikin Hajjin bara wajen tsugunnar da mahajjata 43,000, su ne tantunan da Najeriya ta yi amfani da su ga mahajjata 95,000 yayin aikin hajjin bana.
“Saboda rashin isassun tantuna, yawancin mahajjata da suka yi burin gudanar da aikin Hajji cikin kwanciyar hankali da jin daɗi, sun ƙare da samun kansu cikin rana tsawon kwanaki.
“Mutane da yawa ba su san cewa mafi girman abin da za mu iya yi a matsayinmu na hukumar aikin Hajji shi ne kawai yin korafi ba. Ba mu da wani iko a kan lamarin.